Labaran Duniya

Labaran Safiyar Alhamis 23/11/2023CE Daidai da 09/05/1445AH Ga Takaitattun Labaran Duniya

Kanun labarai Alhamis

Shugaba Tinubu ya yi alhinin mutuwar mutum 17 a hatsarin mota a jihar Neja.

Shugaba Tinubu ya dawo Abuja daga Berlin, kasar Jamus a daren Laraba bayan halartar taro.

Sojoji sun ceto mutane 31 da aka yi garkuwa da su a jihar Sokoto.

Akalla mutum 3 ne suka mutu bayan harin da ‘yan bindiga suka yi a garin Kaura Namoda a jihar Zamfara.

Kotun daukaka kara ta gyara kwafin hukuncin da ta mikawa lauyoyin NNPP a Kano.

Jami’an tsaro sun damke wasu mutane da ake zargin sun fito yin zanga-zanga saboda hukuncin zaben gwamnan jihar Kano.

Gwamnatin Jihar Neja ta yi barazanar katse wutar lantarkin da take bai wa kasar nan muddin ita ma ba a fara bata kaso 13 na kudaden wutar lantarkin da ake samu daga tashoshin samar da wutar da suke jihar ta ba.

Jihohi 36 da ake da su a Najeriya sun batar da N1.71tr a kan alawus, tafiye-tafiye zuwa kasashen ketare a shekarar nan ta 2023.

A wani abu da ya ja hankulan mutane, mata sama da dubu 1 sun fito zanga zanga tsirara a jihar Anambra kan kashe kashe da ya addabi garin Awka.

Kotun majistare dake Abakaliki a jihar Ebonyi a ta daure Chikodili Igboji mai shekara 29 a kurkuku bisa laifin yi wa mata mai shekaru 50 fyade.

Kamaru ta karbi kashin farko na rigakafin maleriya.

Gwamnatin Jamhuriyar Congo za ta binciko abin da ya haifar da mutuwar mutum 37 a wani filin wasa.

Harin ‘yan ta’adda ya kashe mutane 15 a gabashin Burkina Faso.

Kotun Isra’ila ta kori ƙarar neman soke yarjejeniyar tsagaita yaƙi a Gaza.

Uganda za ta yi bincike kan baƙuwar cutar da ta kashe mutum 12.

An kori jaruma daga fim saboda wallafa sakon goyon bayan Falasdinawa.

Kociyan Argentina Scaloni zai yi murabus.

Labaran Yammacin 22/11/2023CE – 08/05/1445AH Ga Takaitattun Labaran Duniyar. 

NNPP ta shigar da kara gaban Kotun Koli kan shari’ar gwamnan Kano.

Ministan Abuja, Nyesom Wike ya bukaci yan adaidaita da su fara tattara komatsansu.

Tsohon mataimakin gwamnan jihar Neja, Ahmed Musa Ibeto da wasu jiga-jigan jam’iyyar PDP sun sauya sheka zuwa APC.

Kwamishinan shari’a ya yi ikirarin NNPP aka ba gaskiya a kotun daukaka kara a shari’ar zaben Gwamnan Kano.

Zanga-zanga ta barke a Kano kan hukuncin Kotun Daukaka Kara na zaben gwamna.

Rahotanni daga birnin Tarayyar Najeriya, Abuja na cewa an yi garkuwa da wasu mata takwas a yankin Kuje.

Sojoji sun ceto mutum 31 da aka yi garkuwa da su bayan sun kai samame mabuyar yan ta’adda a karamar hukumar Tagaza da ke jihar Sokoto.

Kungiyar ma’aikatan shari’a JUSUN reshen jihar Osun ta ayyyana shiga yajin aikin sai baba ta gani ranar Laraba.

Babbar kotun FCT Abuja ta bada belin tsohon gwamnan CBN, Emefiele kan N300m.

Bayan shekaru takwas wata babbar kotu da ke Ikeja, jihar Legas, ta yanke wa wani hukuncin kisa bisa kama shi da laifin kashe jami’an DSS guda 7

Wani mummunan hatsarin motar tirela ya yi ajalin mutane akalla 17 tare da jikkata wasu a jihar Neja.

Rahotanni sun bayyana cewa an yi musayar wuta tsakanin sojoji da ‘yan sanda a Adamawa.

Dan majalisar Ghana ya nemi afuwar Maguire kan zolayar da ya yi masa a bara.

Dakatar da yaki a Gaza zai fara aiki daga karfe 10 na safe a gobe.

An zargi sojojin Sudan ta Kudu da kai hari kan fararen hula a Abyei.

Ƴan bindiga sun kashe mutum 9 a wata kasuwa a Kamaru.

Koriya ta Kudu ta dakatar da yarjejeniyar soji tsakaninta da ta Koriya ta Arewa.

Ambaliya ta kashe mutane 50 a Somaliya tare da raba dubu 700 da muhallansu.

Koriya ta Arewa ta harba tauraron dan adam na leken asiri sararin samaniya.

ADDDINI NASIHA NE

Kada Ka BUƊE ƙofar Da Take Cutar Da Kai, Ko Da Kuwa Mai ƙwan ƙwasawar Wanda Kake Mutuƙar So Ne”

Show More

bibzaria

Ibrahim Salisu Known as Bibzaria CEO of Nhausa for India Hausa, Freelance writer who has written Some of articles over the last decade, covering every conceivable subject from the Indian Hausa Movie

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button