Labaran Duniya

Labaran Duniya na Yau Litinin 27/11/2023 – 12/05/1445 Jerin Takaitattun Kanun Labaran Duniyar

Labaran Duniya na yau BBC Hausa

Ministan shari’a Lateef Fagbemi (SAN) ya bukaci ‘yan kasa da su goyi bayan ayyukan gyara kasa na Shugaba Tinubu.

Haramta holewa a gidan Gala da sauran wuraren rage dare da Hukumar Hisbah ta ce suna kara habaka ayyukan lalata ya janyo cece kuce a Jihar Jigawa a tsakanin wadanda haramcin ya shafa.

Akalla mata dubu ne su ka yi zanga-zanga a titunan garin Kano domin nuna rashin jin dadinsu game da hukuncin shari’ar zabe.

Gwamna Alex Otti na jihar Abia ya watsar da sabon gidan gwamnatin jihar na biliyoyin nairori tun bayan hawanshi mulki inda yake gudanar da mulki daga kauye.

Bayan ‘yan bindiga sun sace mai sarautar gargajiya a yankin Otulu a jihar Imo, daga bisani an tsinci gawarsa a bakin hanya.

An sako wani dan Jamus da ake garkuwa da shi a Mali.

Dubbai mutane sun yi tattaki kan nuna wa yahudawa kiyayya a Landan.

Kasashe na kiraye-kirayen ganin an tsawaita yarjejeniyar Isra’ila da Hamas.

EPL: Manchester United ta sami nasara akan Everton da ci 3:0 a wasan jiya.

Laliga: Real Madrid ta sami nasara akan Cadiz da ci 3:0 a wasan jiya.

Seria A: Juventus da Inter Milan sun tashi 1:1 a wasan jiya.Labaran duniya na Lahadi 26/11/2023 – 11/05/1445AH

Kotu ta bada dama Ajaka da SDP su binciki kayayyakin zaɓen Kogi.

CBN ya umarci bankuna su ƙara narka jarin kuɗaɗe a bankunan su har a kai gejin Dala Tiriliyan 1.

Kotu a birnin kudun jihar Jigawa ta yanke wa Sagir da ke yin lalata da almajirai ta dubura hukuncin ɗaurin rai da rai.

Gogarma Damina ya kwashe sama da mutum 100, bayan an kasa haɗa masa harajin Naira miliyoyin kudin haraji a ƙauyen Matunji a jihar Zamfara.

Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido, ya ƙaryata zargin cewa shi ne ya ƙaƙaba ɗan cikinsa, Mustapha, a takarar Gwamnan Jihar a zaben 2023.

Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani ya shawarci mutane da su rike Alkur’ani hannu bibbiyu don samun zaman lafiya a kasar.

Isra’ila ta saki fitacciyar Bafalasdiniya Israa Jaabis amma ta hana a yi murna.

An kammala shirye-shiryen gudanar da wasan karshe na dambe a Kano.

Kungiyar Hamas ta ce ta kammala sakin ‘yan kasar Thailand da ta yi garkuwa da su a Gaza saboda sanya bakin da shugaban Turkiyya.

Sojojin Mali sun daƙile wasu hare-haren Alƙa-ida.

Qatar ta ce Hamas ta saki yara takwas da mata biyar ga Isra’ila.

Dubban mutane sun gudanar da zanga-zanga a Landan dan nuna goyon bayan Falasdinawa.

Wolverhampton Wanderers na son aron golan Arsenal Aaron Ramsdale a watan janairu.

EPL: Arsenal ta sami nasara akan Brentford da ci 1:0 a wasan jiya.

Laliga: Atlentico Madrid ta sami nasara akan Mallorca da ci 1:0 a wasan jiya.

Seria A: Milan ta sami nasara akan Fiorentina akan da ci 1:0 a wasan jiya.

 

ADDINI NASIHA NE

Idan kana iya karanta wannan sakon to ka kara gode wa Allah domin akwai miliyoyin mutane a duniya da ba su da wannan ni’imar.

BARKANMU DAI

Show More

bibzaria

Ibrahim Salisu Known as Bibzaria CEO of Nhausa for India Hausa, Freelance writer who has written Some of articles over the last decade, covering every conceivable subject from the Indian Hausa Movie

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button