Labaran Duniya

Ana Tsaka Da Yin Mata Allurar Zubar da Ciki ta Mutu – Dan Uwansa ne Yayi Cikin

Labaran Duniya Kaitsaye Daga Kafar Nhausa.com.ng

Jami’ai Sun Chafke matashin da ake zargi ya ‘Dirkawa ƴar’uwarsa ciki amma ta mutu wajen zubarwa

‘Yan sandan Najeriya ta jihar Kano ta ce ta kama wani likitan bogi mai suna Chidera Ugwu bisa zarginsa da yi wa wata mai juna biyu allura lamarin da ya yi sanadin mutuwar ta.

Acikin Sanarwa da rundunar ta fitar, tana ce ta kama likitan ne bayan samun wani rahoto kan wani matashi Ukasha Muhammad mai shekara 19 a ƙauyen Langel da ke ƙaramar hukumar Tofa, wanda ake zargi yi wa Yar’uwarsa ciki, amma ya haɗa baki da Chidera domin yi wa matashiyar allura da nufin zubar da cikin.

Sai dai a cewar sanarwar, an samu akasi inda allurar da Chidera ya yi wa matashiyar ta yi sanadin mutuwarta. A cewar rundunar, matasan biyu sun amsa laifin da ake zarginsu da aikatawa. Ko da yake, BBC HAUSA a karan kanta ba ta iya tabbatar da hakan ba.


Kalli Video Kaitsaye Anan


Sanarwar ta ce ana zargin Chidera Ugwu ya saba yi wa mata masu ciki allurar da take haddasa mutuwarsu, kamar yadda binciken da rundunar ƴan sandan ta ce ta yi ya nuna.

Rundunar Yan Sanda ta kuma ce ta kama wani matashi Yusuf Haruna daga ƙaramar hukumar Dala wanda ake zargi da kashe wani fitaccen limami ta hanyar da’ba masa wuk’a.

Matashin ya daba wa limamin mai suna Mallam Sani Mohammed Shuaibu wuƙar ne a bayansa a lokacin da yake alwala. A cewar sanarwar, an garzaya da limamin asibitin ƙwararru na Murtala Muhammad inda kuma likita ya tabbatar ya mutu saboda ciwon da ya ji. Sanarwar ta bayyana cewa matashin ya yi aika-aikar ne saboda yadda limamin ya sha gargaɗinsa da ƴan tawagarsa kan su daina busa tabar wiwi a harabar masallaci.

Runudnar Yan Sanda ta ce za ta gudanar da bincike kan laifukan biyu domin tabbatar da adalci ga wadanda suka rasa rayukansu.


Share us News on:

Nhausalabarai@gmail.com

Join Our Social Media Channels:

bibzaria

Ibrahim Salisu Known as Bibzaria CEO of Nhausa for India Hausa, Freelance writer who has written Some of articles over the last decade, covering every conceivable subject from the Indian Hausa Movie

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button