Labaran Duniya

Labaran Duniya na Yau Alhamis 30/11/2023 – 16/05/1445 Kanun Labarai daga Kaitsaye Anan 

Gwamnatin tarayya za ta karɓi rancen dala biliyan ɗaya don cike gibin kasafin kudi.

Tinubu ya sake naɗa Mele Kyari shugaban kamfanin NNPC.

An sake mayar da Emefiele kurkuku zuwa Janairu 2024 saboda gaza cika ƙa’idar beli.

Mayakan boko haram sun hallaka masu aikin gawayi 11 a jihar Barno.

Ƴan Najeriya sun kashe N2.6tn wajen sayen katin waya da data a cikin watanni tara.

Wasu ‘yan bindiga sun harbe ‘yan sanda biyu da wani matashi har lahira a mahadar Ahiara da ke Karamar Hukumar Ahiazu Mbaise a Jihar Imo.

Wani riƙaƙƙen ɗan daba ya miƙa kansa ga ƴan sandan Kano.

Mutum 2 sun mutu yayinda wasu mutum 8 suka jikkata a wani rikici tsakanin makiyaya da manoma a ƙaramar hukumar Suru ta jihar Kebbi.

Kimanin dalibai 433 a cikin 836 da suka karanta fannin likitanci a jami’o’in ƙasashen waje sun faɗi jarrabawar samun lasisi da cibiyar yi wa likitoci rijista a Najeriya (MDCN) ta shirya.

Hukumar Alhazai ta Kasa (NAHCON) a Saudiyya, ta tarbi Hajiyar Najeriya ta karshe, Kuburat Motolani Oloruntunmi da rashin lafiya ta tsare a kasar.

‘Yan ta’adda sun kai mummunan hari kan rundunar Sojin Burkina Faso.

Libya ta kora bakin haure sama da 200 zuwa kasashen Nijar da Chadi.

An ceto ma’aikatan haƙar ma’adanai 41 da suka yi kwana 17 a ƙarƙashin ƙasa a Indiya.

Wata kotu a Kenya ta ayyana harajin gidaje da cewa ba ya kan doka.

Masu haƙar ma’adinai 11 sun mutu a wani hatsari a Afirka ta Kudu.

An fara shari’ar matar tsohon shugaban kasar Zambia Esther Lungu.

Ambaliyar ruwa ta mamaye yankuna 38 na kasar Kenya.

Najeriya na duba yuwuwar sallamar kocin Super Eagles.

A yau Talata za a dawo Gasar Champions League bayan gajeran hutun da aka je.


Assalamualaikum barkammu da warhaka fatan kowa yana lafiya inai muku fatan alkairi


SHIN DAN UWA KA YARDA CEWA KOMI NA RAYUWA SAI KANA DA RABO ACIKI KAFIN KA SAMETA ?

kamar yadda mukeji diga bakin malai duk abunda za ka gani arayuwa kuma ya burge ka, ka ji kuma kana bukatar wannan abun to fa lalle sai kana da rabo aciki kafin ka samu wannan abunda kake bukatarsa.

Shin dan uwa ka, san da cewa muddin idan kana da rabo akan abu to fa lalle za ka sameshi ko da kuwa ba ka kusa dashi ko da kuwa yafi karfinka domin kuwa komi lokaci ne.

Idan kuma ya kasance ba rabonka bane to fa lalle bara ka sameshi ba sannan kuma wayorka barai sa ka sameshi ba iliminka bare sa ka sameshi ba domin ba ka da rabo aciki. Allah ya kan azurta bawansa ta hanyoyi daban daban mu kwantar da hankalimmu idan mun yarda da hakan.

Damammaki ba ya karewa a rayuwa idan ka rasa wata dama muddin kana raye, ba abun mamaki bane ka ga Allah ya sake sada ka da wasu damammaki na rayuwa, duk abunda baka sameshi a lokacin da kake bukatarsa ba to ka yi hakuri akwai wata dama da zata sake samunka.

Kar ka bari sannan kuma kar ka yarda zuciyarka ta raya maka cewa idan ka rasa dama ta farko to ka rasa ta kenan arayuwarka wannan ba haka bane.

Idan ka yarda da cewa komi na rayuwa sai kana da rabo aciki kafin ka sameshi to fa lalle ya kamata ka kwantar da hankalinka wuri daya ka ci gaba da addu,a Allah ya sada ka da taka rabon sannan kuma ka jajirce akan ayyukanka na rayuwa.

Idan Allah yasa kana da halin mallakan wani abu na rayuwa to ka mallakesa, idan kuma Allah yasa ba ka da halin mallakan wani abu na rayuwa to fa lalle kar ka takura kanka wurin ganin sai ka mallakeshi.

Domin ba yinka bane yin Allah ne idan ya baka wannan damar to fa lalle za ka mallakeshi.

Show More

bibzaria

Ibrahim Salisu Known as Bibzaria CEO of Nhausa for India Hausa, Freelance writer who has written Some of articles over the last decade, covering every conceivable subject from the Indian Hausa Movie

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button