Labaran Duniya

Takaitattun Labaran Duniyar na Yau Lahadi daga Shafukan Gidajen Jaridu Nigeria – BBC Hausa

Labaran Duniya BBC Hausa bayani

‘Yan bindiga sun bukaci karin babura guda biyu bayan karbar kudin fansa har naira miliyan 10 bayan sun sace mutane 23 a kauyen Kudiri da ke karamar hukumar Kagarko a jihar Kaduna.

Masu zanga-zanga sun ce zaman Wike a kujerar Minista zai kawowa Bola Tinubu matsala a gwamnati.

Mukaddashiyar Kwamandan Hukumar EFCC ta Kaduna Aisha Abubakar ta jagoranci tattakin Ranar Yaki da Rashawa ta Duniya a jihar.

Gamayyar lauyoyin arewacin Najeriya na shirin maka gwamnatin tarayya a gaban kotu kan harin Kaduna.

An yi wa tsohon shugaban kasar Sierra Leone Koroma daurin-talala.

Mayakan Houthi sun sha alwashin hana jiragen ruwan daukar kaya shiga Isra’ila

Gwamnatin Ghana na shirin karkatar da akalar bautar kasa zuwa bada horo kan aikin gona.

Shugaban Falasɗinawa Abbas ya ɗora alhakin ‘kisan yaran Gaza’ a kan Amurka.

Al’ummar Masar zasu kada kuri’a a babban zaben kasar yau Lahadi.

Ɗan wasan Manchester City Kalvin Phillips, na cikin ƴan wasan farko da Manchester United za ta yi cefane.

EPL: Aston Villa ta sami nasara akan Arsenal da ci 1:0 a wasan jiya.

Laliga: Real Soceidad ta sami nasara akan Villarreal da ci 3:0 a wasan jiya.

Seria A: Atalanta ta sami nasara akan Ac Milan da ci 3:2 a wasan jiya.

Seria A: Inter Milan ta sami nasara akan Udinese da ci 4:0 a wasan jiya.

Ga Takaitattun Labaran Duniyar.

Shugaba Tinubu ya bada umarnin sake gina kauyen Tudun Biri dake jihar Kaduna.

Shugaba Tinubu ya mika sakon ta’aziyya ga Sarki Salman na kasar Saudiyya kan mutuwar Yarima Talal bin Abdulaziz bin Bandar Al Saud.

Najeriya na nazarin mika harkokin samar da wutar lantarki ga gwamnatocin jihohi.

DSS za ta fara amfani da makaman da jami’anta suka ƙera.

Kamfanin NNPC ya ce ya gano bututan mai haramtattu har 4,800 zuwa matatun mai daban-daban a ƙasar.

Sheikh Yabo ya ce ko sau daya sojoji ba su taba sakin bam a yankin Yarabawa da Inyamurai ba.

Gwamnan jihar Kebbi ya amince da biyan kuɗin giratuti ga ma’aikata 745 da suka yi ritaya ko suka rasu a jihar.

Kungiyar Lauyoyi Masu Kishin Arewa na shirin maka gwamnatin tarayya a kotu domin neman hakkin mutanen da jirgin soja ya jefa wa bom a jihar Kaduna.

Sarkin Katsina, Abdulmuminu Kabir, na shirin korar shirin nan na inganta ilmin ’yan mata mai suna AGILE daga fadin jihar. Sarkin ya ce, shirin na AGILE yana wuce gona da iri da kuma kokarin gurbata tarbiyyar Musulunci da ta al’ada da aka san yankin da ita.

Aƙalla masu haƙar ma’adanai mutum 3 ne suka rasu yayin da 11 suka samu raunuka sakamakon ruftawar wani ramin haƙar ma’adinai a kauyen Dan Kamfani da ke ƙaramar hukumar Anka ta jihar Zamfara.

‘Yan sandan Landan sun kama mutum a wurin zanga-zangar goyon bayan Falasɗinawa daya kwatanta Isra’ila da Gwamntain Nazi ta Jamus.

An kashe ɗan Isra’ila da ake garkuwa da shi a Gaza.

Jakadiyar Amurka za ta gana da Tinubu da Ecowas kan matsalar Nijar.

An yanke wa wani matashi hukuncin ɗaurin rai da rai a Amurka bayan samunsa da laifin harbe wasu ɗalibai huɗu a 2021.

Kungiyoyin fararen hula sun bukaci ECOWAS ta haramta yin wa’adi na 3 a Mulki.

An yanke wa tsohon Firaministan Burundi hukuncin daurin rai-da-rai.

EPL: Liverpool ta sami nasara akan Crystal Palace da ci 2:1 a wasan yau.

Laliga: Real Betis da Real Madrid sun tashi 1:1 a wasan yau.

Frankfurt ta sami nasara akan Bayern Munich da ci 5:1 a wasan yau.

EPL: Bounemouth ta sami nasara akan Manchster United da ci 3:0 a wasan yau.

Show More

bibzaria

Ibrahim Salisu Known as Bibzaria CEO of Nhausa for India Hausa, Freelance writer who has written Some of articles over the last decade, covering every conceivable subject from the Indian Hausa Movie

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button