Labaran Duniya

Labaran Safiyar Lahadi 05/11/2023CE – 21/04/1445AH Ga Takaitattun Labaran Duniyar. 

Hausa News Nigerian Latest News Hausa Newspaper

Kotun daukaka kara, dake Legas, ta kori Darlington Nwokocha, bulalan marasa rinjaye a majalisar dattawa, mai wakiltar Abia ta tsakiya a karkashin jam’iyyar (LP).

Gwamnan Kaduna Uba Sani ya biya tulin bashin kudin wutar lantarkin Jami’ar KASU na tun daga 2022.

Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi ya amince da biyan naira miliyan 497 na jarabawar WAEC ta 2023 ga dalibai a jihar.

Hukumar NSIB ta kaddamar da bincike kan hatsarin jirgin sama da ya ritsa da ministan wutar lantarki.

Yahudawa na zanga zangar neman tsagaita wuta a Gaza domin kubutar da ‘yan uwansu.

Kungiyar Hezbollah ta ce ta kashe sojojin Isra’ila da dama a arewacin kasar don yin raddi kan kisan da dakarun Isra’ila suka yi a Lebanon.

Ofishin jakadancinAmurka a Najeriya ya shawarci Amurkawa da su yi taka-tsan-tsan yayin yada zango a manyan otal a manyan biranen kasar.

Shugaban Ukraine ya ce yaƙin da ake yi tsakanin Isra’ila da Gaza ya ”ɗauke hankali duniya” daga yaƙin da ake yi a ƙasarsa.

Sojojin mulkin Guinea sun ce an mayar da tsohon shugaban ƙasar Moussa Dadis Camara gidan yari.

Masar ta jaddada kiran tsagaita wuta ‘nan take’ a Gaza.

NPP ta tsayar da Mahamudu Bawumia takarar shugaban kasar Ghana.

Labaran Kwallon kafa

Manchester United na shirin musayar dan wasa Antony, mai shekara 23, da dan wasan gaba na Gabriel Barbosa daga Flamengo.

EPL: Newcastle ta sami nasara akan Arsenal da ci 1:0 a wasan jiya.

Laliga: Barcelona ta sami nasara akan Sociedad da ci 1:0 a wasan jiya.

Seria A: Inter Milan ta sami nasara akan Atalanta da ci 2:1 a wasan jiya.

Bundesliga: Bayern Munich ta sami nasara akan Dortmond da ci 4:0 a wasan jiya.

Show More

bibzaria

Ibrahim Salisu Known as Bibzaria CEO of Nhausa for India Hausa, Freelance writer who has written Some of articles over the last decade, covering every conceivable subject from the Indian Hausa Movie

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button