Labaran Duniya

Labaran Safiyar Juma’a 17/11/2023CE – 03/05/1445AH Ga Takaitattun Labaran Duniyar.

An baza karin sojoji da ‘yan sanda a Kano gabanin hukuncin kotu kan shari’ar Abba da Gawuna.

A safiyar yau Juma’a ne kotun daukaka kara za ta yi hukunci a kan zaben Gwamna na jihar Kano a Abuja.

Jam’iyyar NNPP tace Ganduje da Abdullahi Abbas sun shirya tayar da tarzoma a Kano.

Mai ba Shugaban Kasa Shawara kan Harkokin Tsaro, Nuhu Ribadu, ya ce matsalolin tsaro sun ja baya a fadin kasa tun da Tinubu ya karbi mulki.

Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke Abuja ta soke zaben Gwamnan Jihar Zamfara da INEC ta bayyana Dauda Lawal a matsayin wanda ya lashe, ta kuma ce a sake zabe a Kananan Hukumomi uku na jihar.

A yau Juma’a ne Alkalan Kotun daukaka kara za su zartar da hukunci a kan shari’ar zaben Gwamnan jihar Bauchi.

Mutane da dama sun rasa rayukansu bayan fada ya barke dalilin harin ‘yan bindiga a karamar hukumar Tangaza a jihar Sokoto.

Kotun masana’antu ta Tarayya ta dakatar da Gwamna Ademola Adeleke daga daukar mataki kan shugabar alkalan jihar.

Fitaccen jarumin Kannywood Abdallah Amdaz ya ce babu wanda ya isa ya sanya shi ya janye kalamansa na zargin ’yan Kannywood da lalata tarbiyya.

Mutum 11 sun shiga hannu kan zargin garkuwa da mutane da kuma yi wa masu garkuwa da mutane leken asiri a sassan Babban Birnin Tarayya.

Shugaban bangaren siyasa na Hamas Ismail Haniyeh ya ce za su murkushe dakarun Isra’ila a Gaza, kamar yadda suka yi shekaru 18 da suka gabata.

Ƴan sandan Kenya sun bankaɗo wata gagarumar damfara a Nairobi.

An maka fitaccen mawakin zamani na Amurka Sean Combs da ake kira P. Diddy a kotu kan zargin fyade da cin zarafin mawakiya Cassandra Ventura wacce aka fi sani da Cassie.

Bankin Raya Afirka ya ce an ci zarafin ma’aikatansa a Habasha.

Sojojin Isra’ila sun ce sun gano gawar wata da aka yi garkuwa da ita a Gaza.

FA ta tuhumi Arteta kan kalamansa bayan wasan Newcastle.

Florenzi na fuskantar bincike kan harkar caca.

ADDINI NASIHA NE

Duk wanda zuciyarsa take tuna masa yawan zunubansa kuma ta tsorata shi da tuna mutuwa, hakika yayi babban rabo, ba abunda ya rage masa face ya yawaita Istighfari da kokarin kyautata ayyuka da addu’ar kyakykyawar cikawa.

BARKANMU DA JUMMA’A

Show More

bibzaria

Ibrahim Salisu Known as Bibzaria CEO of Nhausa for India Hausa, Freelance writer who has written Some of articles over the last decade, covering every conceivable subject from the Indian Hausa Movie

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button