Labaran Duniya

Labaran Safiyar Alhamis 16/11/2023CE – 02/05/1445AH Ga Takaitattun Labaran Duniyar. 

Labaran Duniya na yau - BBC Hausa Shirin Safe

Kungiyoyin kwadago sun sanar da janye yajin aikinsu.

Majalisar Dattawa ta yi barazanar cefanar da hukumar kula da gidajen waya ta kasa (NIPOST), saboda rashin samar da kudaden shiga da ya kamata ga Gwamnatin Tarayya.

Gobara ta tashi a wani sansanin ƴan gudun hijira a Borno.

An shiga wani irin yanayi bayan tsintar gawar lakcara a Jami’ar Obafemi Awolowo, OAU da ke jihar Osun.

An cafke mutum 11 kan garkuwa da mutane a Abuja.

‘Yan sanda a Kaduna sun kama wani matashi bisa zargin kashe mahaifinsa da tabarya bayan ya zuciyarsa ta kaddara masa cewa uban na yunkurin halaka shi.

Mawaƙin Najeriya Oladips ya mutu yana da shekara 28.

Kwamitin Sulhu ya amince da ƙudurin dakatar da yaƙi a Gaza.

Gwamnatin Birtaniya ta sha kaye a kotun ƙoli kan batun tura ƴan ci-rani Rwanda.

Sakamakon farko na zaɓen shugaban ƙasa zagaye na biyu a Laberiya na nuna cewa an yi fafatawa mai zafi.

An kashe karin sojojin Isra’ila biyu tare da jikkata wasu biyu a gumurzun da ake yi a Zirin Gaza, a cewar kafar watsa labarai ta gwamnatin Isra’ila.

Za a binciki Chelsea kan wasu kudi da ta biya lokacin Abromovich.

El-Ghazi ya shigar da ƙara kan sallamarsa daga Mainz kawai dan yayi magana akan Isara’ila.

Labaran Yammacin Laraba 15/11/2023CE – 01/05/1445AH Ga Takaitattun Labaran Duniyar.

Shugaba Tinubu na shirin ganawa da shugabannin ƙasashen duniya a birnin Bissau na ƙasar Guinea domin halartar bikin cikar kasar shekara 50 da samun ‘yancin kai.

Gwamnatin tarayya ta shiga ganawa da kungiyar kwadago don neman hanyoyin da za a bi don kawo karshen yajin aikin da kungiyoyin suka shiga.

Mai ba wa Shugaban Kasa Shawara kan Tsaro Nuhu Ribadu, ya ba wa Kungiyar Kwadago hakuri tare da neman su janye yajin aikin da suka fara.

Jami’ar Bayero ta Kano ta dakatar da jarabawar zangon farko shekarar 2022/2023 sakamakon yajin aikin da kungiyar kwadago ta fara.

Wata mata mai suna Shamsiyya Yunusa ta nemi Kotun Shari’ar Musulunci da ke zamanta a Filin Hockey a Jihar Kano da ta nema wa danta mahaifi daga cikin maza biyun da ta rabu da su.

Mutum 4 sun mutu wasu sun jikkata a hatsarin mota a jihar Abiya.

Kotun Ɗaukaka Ƙara ta kammala sauraron shari’ar zaɓen gwamnan Nasarawa.

Majalisar Dattawa ta rantsar da Austin Akobundu na jam’iyyar PDP da ke wakiltar Abia ta Tsakiya a Majalisar bayan yayi nasara a kotu.

Wasu da ake zargin barayi ne a yau sun sace wayar tsohon Ministan Watsa Labarai, Labaran Maku a kotun daukaka kara da ke Abuja.

Shugaba Erdogan na Turkiyya yace kasar sa za ta tabbatar wadanda ke da hannu a kisan kiyashin Gaza sun fuskanci shari’a.

Gwamnatin Ghana ta amince ta karawa ma’aikata albashin da yawansa ya kai kashi 23.

An tsare ‘Yan jaridun Togo biyu saboda zargin minista.

‘Yan majalisar dokokin Uganda sun amince a kawo karshen shigar da mai ta Kenya.

Majalisar Dinkin Duniya za ta koma kai kayan agaji ta sama zuwa Nijar.

Shugaban Sudan ta Kudu ya kori shugaban ‘yan sanda bayan jita-jitar juyin mulki.

Babban jami’in Manchester United, Richard Arnold zai sauka daga muƙaminsa wanda shine ya maye gurbin Ed Woodward a matsayin mai babban muƙamin mahukuntan ƙungiyar a watan Fabrairun 2022.

Show More

bibzaria

Ibrahim Salisu Known as Bibzaria CEO of Nhausa for India Hausa, Freelance writer who has written Some of articles over the last decade, covering every conceivable subject from the Indian Hausa Movie

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button