Labaran Duniya

Labaran Laraba 08/11/2023CE – 24/04/1445AH Ga Takaitattun Labaran Duniyar.

Hausa News BBC Hausa Labaran Duniya

Majalisar Najeriya tace Kashe rayuka da karya dokokin yaƙi a Gaza, dole su yi magana.

Kotun ɗaukaka ƙara ta ce Lalong ne ya lashe zaɓen sanata a Filato.

Masu garkuwa da mutane sun sako matan Shugaban Karamar Hukumar Kiyawa, Nasiru Ahmad na Jihar Jigawa su biyu.

Hukumar FRSC reshen Jihar Gombe, ta ce mutum 79 ne suka mutu a hatsarin mota 278 da suka faru daga farkon watan Janairu zuwa 31 ga Oktoban 2023.

Babbar kotun tarayya da ke Ibadan ta yanke wa wani manomi hukuncin daurin shekara shida kan laifin noma da kuma ta’ammali da tabar wiwi.

Akalla mutum 4 ne suka rasa rayukansu a wani hatsarin kwale-kwale a karamar hukumar Awe da ke jihar Nasarawa.

Hisbah ta kori jami’inta kan hada kai da masu badala a Kano.

Kiristocin Gaza na zaman fargaba sanadiyyar rikicin Isra’ila.

An soke ziyarar da Firaiministan Czech zai kai Nijeriya saboda ‘ba za a iya daukar dawainiyarsa ba’

Za a yi taron kasashen Musulmai da na Larabawa a Saudiyya kan yakin Gaza.

Afirka ce ke dauke da sama da kaso 30 ‘yan gudun hijirar duniya, inda Uganda kaɗai ke da da adadin da ya haura jama’ar wasu kasashen nahiyar.

Labaran Wasanni

Wakilin Antony na Manchester United ya ce ba zai yarda a yi musayarsa da Gabriel Barbosa daga Flamengo ba.

Manchester United ta matsu da cinikin Todibo daga Nice, domin maye gurbin Raphael Varane, da ke shirin tafiya Saudiyya.

UCL: Shakhtar ta sami nasara akan Barcelona da ci 1:0 a wasan jiya.

UCL: Ac Milan ta sami nasara akan PSG da ci 2:1 a wasan jiya.

UCL: Manchester City ta sami nasara akan Young Boys da ci 3:0 a wasan jiya.

UCL: Atlentico Madrid ta sami nasara akan Celtic da ci 6:0 a wasan jiya.

Show More

bibzaria

Ibrahim Salisu Known as Bibzaria CEO of Nhausa for India Hausa, Freelance writer who has written Some of articles over the last decade, covering every conceivable subject from the Indian Hausa Movie

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button