Social Media

Ga Wanda Basu san menene CAC ga Bayanin CAC Atakaice (Corporate Affairs Commission)

C.A.C Na nufin Corporate Affairs Commission Ma'ana Hukumar kula da harkokin Kasuwanci .

Menene C.A.C ?

A kamfanin ALBADAR GLOBAL AGENCY LTD Zamu taimaka muku, ku mallaki Rijistar CAC ta Kamfanin ku..

C.A.C Na nufin Corporate Affairs Commission Ma’ana Hukumar kula da harkokin Kasuwanci .

An kirkireta a shekarar 1990 a bisa sahalewar kudurin sashin doka na CAMA wanda Yan Majalisar dattawa suka amincewa. Aikin ta shi ne samar da cikakkun bayanan Industiri din kasa (Company) da kuma tabbatar da lasisi ga kowacce ma’aikata hada da kididdige adadin kamfanoni da kuma matsakaitan yan kasuwa.

Hukumar ta hada wakilai ta ɓangarori da dama kamar

  • Kungiyar ma su samar da Abubuwa ta kasa Manufacturers Association Of Nigeria (MAN) .
  • Kungiyar Manyan Ma’aikatan banki ta kasa Instute Of Chartered Accountants Of Nigeria (ICAN) .
  • Kungiyar Lauyoyi Ta Kasa Nigerian Bar Association (NBA).
  • Kungiyar Manyan Yan Kasuwar Harkokin Noma da Kiwo Hadi da Sarrafa Ma’adanai Ta Kasa Nigerian Association Of Chambers of Commerce Industry Mines And Agriculture (NACCIMA) .
  • Ma’aikatar Kula da Kasuwanci Da Yan Kasuwa Ta Kasa Federal Ministry Of Industry, Trade , and Investment (FMITI) .
  • Kungiyar wakilan Tsaro da Jami’an Canji Ta Kasa Securities & Exchange Commission (SEC).
  • Hukumar Shari’a Ta Kasa

Rabe-raben Aikace-aikacen ta

  • Daukar Ma’aikata
  • Rijistar Kasuwanci
  • Rijistar Kamfani Da Hadakar Yan Kasuwa .

Wannan rabe-raben ya hada da dukkanin wadannan aikace-aikacen .

  • Samar da Lasisin Kamfani na Jama’a
  • Rijistar sunan kasuwanci
  • Rijistar Hadakar Jama’a
  • Rijistar Sana’a Ko Haja Ta Kwana Daya
  • Daukar Bincike
  • Fitar da Ingantaccen Bayanan Kasuwanci
  • Rijistar Hannun Jari Ko Gidaje
  • Samar da bayanan shige da ficen kasuwanci a Shekara
  • Shirya Bincike a Ma’aikatu da kamfanoni Akan ƙorafin da aka shigar
  • Sayar da bayanai na ka’ida
  • Sa Hannun Akan abinda Ya shafi Ɓangaren Kudi Ko Shari’a

Ire-iren Aiki

Akwai ire-iren Hanyoyin da ake gane Kamfani Guda Hudu

Private Limited Company (LTD)

Public Limited Company (PLC)

Company ɗin da ya samu Sahalewa

Da Company Mara Sahalewa

Mafi karancin Mutanen da ake so a hadakar kowanne kamfani Cikin Su Mutum Biyu .

Private Company PLC kuma Mafi yawa ya dauki mutum 50 , Ya yin Da Shi Kuma Public Limited Company Ba a Kayyade Mutane Ba .

Kamfani na nufin shaida ta hadin kai , abun da Babu Hadin kai zai Kasance a Rabe .

Dokar da take Nuni da Yadda Za a yi Rijistar Kamfani a Najeriya ita ce Companies And Allied Matters Act wadda aka Sabun ta ta a 2004 .

Hanyar Da Za Ku Bi Wajen Rijistar Kamfani Naku Da Corporate Affairs Commission (CAC)

Samarwa Kamfani Suna

Matakin farko da za a bi wajen kirkirar kamfani shi ne samar mashi da suna wanda za a rijistar da shi .

Wanda za a Tura ta Website din CAC

Idan an taba rijista da irin Sunan ba za su Karba ba .

Samar Da Cikakkar Sahalewa

wannan na kammaluwa ta wajen Lauya ko kuma Ma’aikacin Shari’a .

Da kuma tabbatar da doka da Oda a kamfanin .

Cike Form din CAC

Idan Shugaban kamfanin daya ne shi kadai zai cike haka idan suna da yawa duk sai sun cike .

  • Biyan Kudin Sitamfi Da Kudin Shigarwa Hadi Kudin Revenue
  • Har Hada Takardun Rantsuwa Da Evidence Na Payment Ko Sitamfi
  • Tura Takardun Ainihi Zuwa Hukumar
  • Document din Da ake bukata Wajen Rijistar CAC
  • Notice Of Registration Address
  • Takardar Sahalewar Ƙungiyoyi (Wato Sahalewa daga Lauya)
  • Shaidar Biyan Kudin Sitamfi
  • Jerin Mamallakan Kamfani
  • Ya Kasance Kamfanin yana da Members Daga 2-50
  • Ya kasance Shekarun Members ɗin Sun Kai 18.
  • Muhimmanci Yiwa Kamfani Rijista
  • Samun kyakkyawar Sahalewa daga Gwamnati
  • Ma’ana kamfanin ka na da damar kai kaya duk inda ya so a Najeriya da kasashen Waje ka akwai kyakkyawar alaka da Gwamnati koda ta shi tai za ta kara ba Masu Kananun Jari , Jari masu Rijista Za su fara Nema .
  • Da samun kwanciyar hankali domin wannan shaida da ka samu daga Gwamnati ita za ta rika saka kayan kamfanin ka shiga ko’ina na duniya .
  • Samun karin kudaden shiga domin samun shaidar kasuwanci shi ke nuna wata manuniya ta cewa Kasuwancin ba na Damfara ba ne za ka ga Mutane ta ko ta ina Suna Bullowa Don Su Saka Jarinsu ko siyan Hajar ka .
  • Kasuwancin ka Zai Samu Daraja da Martaba a Idon Duniya

Za ka samu Kariya Daga Gwamnati

ALBADAR GLOBAL AGENCY LTD Yana Ɗaukar Nauyin Kafa kamfanoni Dakuma Tsarawa da Tallatawa.

Ku tuntuɓe masu yi ta wannan lambar wayar 08086251045

Show More

bibzaria

Ibrahim Salisu Known as Bibzaria CEO of Nhausa for India Hausa, Freelance writer who has written Some of articles over the last decade, covering every conceivable subject from the Indian Hausa Movie

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button