1000+ Hausa Novels

KWARATA Hausa Novel Complete

Download Kwarata Complete Littafin Hausa Novel by Jamila Musa

Page1 Shekaru na goma sha bakwai cas a duniya. Babana yana da mata hudu da ƴaƴa hamsin da bakwai. Mahaifina ya kasance dan auri saki ne, bakin abinda kunne na yaji mahaifina ya auri mata ashirin da takwas.

Babana ya kasance talaka ne baya da wata sana’a wadda ta wuce “yan bige bige, ya gwanance wurin iya karya sannan kuma babu abinda kware dashi sai cin bashi. Talakane amma baya saka sutura irin tasu, idan kika gansa zaki rantse da Allah yana iya kyautar naira miliyan biyar, yasan dadin kudi sosai amma a sutura baya tausawa naira.

Baya da gidan zama haka kuma baya da fili ko taki daya, munyi zama a anguwanni da dama sosai wanda duk anguwar da muka sauka suna mana lakabi da gidan inna ratata, ko kuma suce gidan yawa. Baya da aiki sai shaye shaye sannan kuma duk gidajen cacar dake garin katsina babu inda ba’asan shi ba, ya saka kansa caca wanda ake kira da nigerful, caca ce wacce take cinye tattalin arziki kuma ba kananan talakawa keyinta ba sai masu kudin gaske saboda idan har za’a buga wasan cacar mahaukatan kudine ake zubawa.

Baya bayar da abinci haka kuma babu abinda ya damesa da rashin lafiyar “ya “yansa ko matansa, idan dai caca tayi masa dadi zai siyo kwanon shinkafa daya da kuma rabin doya, Da safe idan zai fita zai bayar da kudin kalaci ko wane daki naira talatin babu wani abinda ya damesa da yawanku. Wata rana can wurin wasan caccarsa aka cisa, amma baya da kudin da zai biya daga cikin abinda aka saka masa, dan haka suka cire masa sutura, tun daga inda ya buga wasan har zuwa gidanmu daga shi sai gajeran wando haka ya ratso mutane saboda tsabar shi tantirine har ya iso gida.  Babu ruwansa da tarbiyar dan sa ko yar sa, shi yasa muka mayar da gidanmu kamar gidan karuwai, domin dai kowa abinda takeso shi takeyi dan babanmu yace sana’a itace tafi cancanta ga duk diyar daya haifa, ya daina biyan kudin haya yace mu zamu rika biya tunda kowa ya kawo karfi, dan haka duk yayuna suka tashi dan neman na kansu kowa ya kama sana’a amma banda ni,

Abinda yasa kuwa shine, lura da irin kyawun da Allah yayi min, karkuyi tunanin kyawu na wasa ko ku lakaba abin da shirme ni nake gaya muku haka, bawai a gidanmu ba gaba daya zuri’armu babu yarinya mai kyau da daukar hankali kamar nawa. Ina da kyau fiye da tunanin mai tunani, ina da diri daidai irin wanda maza ke so, ina da babban kugu sannan kuma Allah ya bani baiwar iya murzasa.

Haka kuma ina da cikar kirji ina da manya idanuwa sannan ina da fari irin na fulanin asali, gaba daya zuri’armu babu mai haske na, idan na shigo taro mata sun gama wali haka kuma babu macen da zata kara tasiri harsai na bar wurin.

Ni “yar gayu ce, na iya wanka kuma na iya shafa turare gaba daya bani da tsara idan na ziyarci wuri kamshina zaiyi ta kasancewa a wurin, haka kuma idan na barsa turarena zai dade bai daina tasiri ba, sannan duk gidanmu babu mai ilimin addini na wanda na samesa ta dalilin mahaifiyata saboda nayi sauka kuma bakin gwargwado nasan hadissai amma gaba daya zuri’armu babu mai barna irin tawa, ga sani ga barna dan duk yanda nake dakai a danginmu idan har na kwallafawa raina saina bata ka tou fa lallai saina bata maka rayuwa.

Ku kasance dani a cikin littafin *KWARATA* domin jin wannan wane irin ubane ita kuma wace irin diya ce ? Kuma a cikin ita da uban waye yafi tantiranci ? Domin dai ni sana’ar da na zabawa kaina itace *KARUWANCI* danni a gani na itace sana’ar da tafi saurin kawo kudi.

Babana mahaifi shine mutum na farko daya fara budemin lasisin karuwanci, domin dai a wurin wasan cacarsa yayi kyauta da budurcina, wannan dalili yasa na zabi sana’ar karuwanci, shine ya fara ni kuma naci gaba da kasancewa da wasan domin dai masu iya magana sunce so da yawa kana koyawa mutum abu amma saiya fika kwarewa.

Ni babban kamfani ce kamar yanda ake sakawa a jikin kayan masarufi ace ingrediants to nima ina da nawa ingrediants in, kamar yanda company yake sarrafa abubuwa to nima company ce mai zaman kaina.

Wannan labari a kiyayi juyashi ta ko wace siga domin yin hakan babban kuskure ne , ba kagoshi nayi ba a haka ta fadamin shi domin ina so ya zama izina ga matan aure.

For Continue Reading

Download Complete Hausa Novels

DOWNLOAD NOW 

You can check Related Hausa Novels

Show More

bibzaria

Ibrahim Salisu Known as Bibzaria CEO of Nhausa for India Hausa, Freelance writer who has written Some of articles over the last decade, covering every conceivable subject from the Indian Hausa Movie

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button